Kasashe masu bada gudumowa sunyi alkawarin kudi ga Haiti | Labarai | DW | 26.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashe masu bada gudumowa sunyi alkawarin kudi ga Haiti

Masu bada gudumowa na kasa da kasa sunyi alkawarin baiwa kasar Haiti dala miliyan 750 domin taimaka mata farfado da tattalin arzikinta.

Wakilan kasashe 40 da cibiyoyin kudi sukayi wannan alkawari wajen wani babban taronsu a babban birnin kasar Haiti.

Wannan gudumowa kuwa ta dara nesa ba kusa,bukatar dala miliyan 540 da sabon shugaban kasar Rene Preval da Firaminista Edourdo Alexis suka mika,domin taimaka gina hanyoyi da makarantu da asibitoci tare da inganta aiyukan yan sanda da fannin sharia na kasar.