Kasashe da dama sun yi alkawarin ba da karo karon sojoji ga runduar MDD a Lebanon | Labarai | DW | 18.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashe da dama sun yi alkawarin ba da karo karon sojoji ga runduar MDD a Lebanon

MDD ta ce kasashe membobin ta sun yi mata alkawarin ba da gudummawar dakaru dubu 3 da 500 ga rundunar kasa da kasa da zata girke a Lebanon. Bangladesh ce ta yi tayin ba da dakaru mafi yawa inda ta ce a shirye ta ke ta tura dakaru dubu 2, to amma Faransa wadda ta ce zata jagoranci tawagar, ta yi tayin ba da dakaru 200 ne kacal. Da farko dai an sa ran cewa Faransa zata ba da gudummawa dakaru masu yawan gaske. Shugaba Jacques Chirac ya ce mai yiwuwa a wani lokaci nan gaba zai kara yawan dakarun ya zuwa sojoji dubu 1 da 700, to amma ba zasu kasance karkashin lemar MDD ba. Tarayyar Jamus kuwa ta kawad yiwuwar ba da na ta sojojin ga rundunar kiyaye zaman lafiyar da MDD zata girke a Lebanon. To amma duk da haka SGJ Angela Merkel ta ce kasar ka iya ba da taimakon kayan aiki da na sojin ruwa a gabar tekun Lebanon.