Kasashe 40 sukayi zanga zangar Allah wadai da fyade a Darfur | Labarai | DW | 10.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashe 40 sukayi zanga zangar Allah wadai da fyade a Darfur

A yau ne a kasashe 40 akayi zanga zangar yin Allah wadai da halin da ake ciki na fyade da tashe tashen hankula a yankin Darfur .

Zanga zangar wadda kungiyoyin mata dana kare hakkin bil adama cikinsu har da Amnesty tazo dai dai da ranar MDD ta kare hakkin bil adama a duniya.

Wajen bikin sakataren MDD Kofi Annan yace abin kunya ga kasashen duniya su zuba ido suna ganin abinda ke faruwa a Darfur

A wani labarin kuma masu sa ido na AU akalla su 8 ne akayi garkuwa da su na dan kankanin lokaci kusa da wani kauye a lardin na Darfur.

Tawagar ta AU tana a yankin don duba halin da ake ciki a Sirba bakin iyakar Chadi inda yan bindiga suka kashe mutane 22 a karshen mako,yayinda jamar kauyen suka bukaci tilas sai sun dauki hotunan wadanda aka kashe tare kuma da hana su su wucewa yankin al janaina.

Yanzu haka dai jamian na AU suna ofishin yan sanda na Sirba inda ake sa ran zasu kawan.