Kasar sin ta yunkura wajen dakile cutar murar tsuntsaye
February 9, 2006Talla
Jami´an kiwon lafiya a kasar Sin sun sanar da killace wasu ma´aikatan gidan gona 15 don gudanar da nazari a kansu.
Hakan kuwa ya biyo bayan rasuwar tsuntsaye ne dubu goma sha biyar wanda keda nasaba da cutar murar tsuntsaye.
A cewar kamfaninin dillancin labaru na kasar, wato Xinhua bullar wannan cuta mai nau´in H5N1 a kasar ya zuwa yanzu ya haifar da kisan tsuntsaye na gida a kalla kusan dubu dari biyu.