1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Sin ta kare harkokin kasuwanci da Afrika

Hauwa Abubakar AjejeMarch 12, 2007

Kasar China ta fito fili tana mai kare harkokin kasuwanci tsakaninta da kasashen Afrika tana mai baiyana cewa kasashen turai da Amurka ya kamata su sake duba harkokinsu a nahiyar kafin suyi suka ga kasar ta China.

https://p.dw.com/p/Btw3
Hu Jintao a Namibia
Hu Jintao a NamibiaHoto: AP

Kasar ta China dai ta saka hannayen jari a Afrika musamman ma dinbin jari na albarkatun mai da take da shi a kasar Sudan,sai dai kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama sunce saka jarinta a Sudan yana kawo cikas ga yunkurin kawo karshen yakin basasa da cin zarafin jamaa a yankin Darfur.

Nahiyar Afrika gabaki dayanta tana a matsayin kashi 1 bisa uku na inda China take samun danyen man fetur,inda kasar angola take kasa data fi fita da manta zuwa China,a nahiyar ta Afrika.

Sai dai ministan ciniki na China Bo Xilai,wajen wani taron manema labarai yace akawai rade rade da ke nuna kamar kasarsa tana da zari a Afrika yana mai baiyana cewa,abinda kasarsa takeyi a Afrika,tana yi ne da zuciya daya saboda abota da zumunci na shekara da shekaru dake tsakaninta da kasashen Afrika.

Ministan na Sin yace duk da suka da wasu kasashe keyi na cewa kasar China tana kwasan albarkatun mai daga nahiyar Afrika,amma a cewarsa alkalumma sun nuna cewa cikin yawan mai da aka fita da shi daga nahiyar Afrika a bara,kashi 8.7 ne kadai ya isa kasar China,nahiyar turai ta kwashi kashi 36 yayinda Amurka ta fita da kashi 33 cikin dari.

Yace idan har fita da kashi 8.7 na yawan mai da afrika take samarwa a shekara yana matsayin zari,to mai zaa ce da kasashen da suka kwashi kashi 36 ko kashi 33 cikin dari.

Kasar ta Sin dai ta maida Afrika a tsakiyar harkokinta na diplomasiya,tana mai bukatar kuma dinbin albarkatun makamashi da wasu albarkatu na nahiyar domin tattalin arzikinta da a kullum yake kara habaka,tare kuma da bukatar goyon bayan kasashe 53 na Afrika a MDD.

A shekarar da ta gabata wajen wani babban taro na kasar ta China da kasashen Afrika a birnin Beijing,shugaban kasar China Hu Jintao yayi tayin baiwa Afrika rancen dala biliyan 5 .

Inda a watan daya gabata kafin ziyarasa zuwa Afrika Hu,ya sanarda cewa kasarsa zata bada rance da babu ruwa cikinsa na dala biliyan 3 ga wasu kasashen nahiyar.

Rangadinsa na kasashe 8 a Afrika ya hada da kasar Sudan inda yayi alkawarin bada rance da babu ruwa na dala miliyan 12 da digo 9 ga sudan din don gina sabuwar fadar shugaban kasa tare da yafe mata bashin dala miliyan 70.

Wadannan taimako da saka jari da China takeyi a nahiyar Afrika ya janyo suka daga kasashen yammacin duniya masu bada gudumowa wadanda suke cewa kasar ta China tana karfafa cin hanci da rashawa da almubazzaranci tunda bata gindaya sharudda wajen bada ranceta ga kasashen na Afrika.

Minisatan na kasar Sin yace suna ci gaba da jin jita jita cewa kasar ta Sin ta zamo sabuwar shugabar mulkin mallaka a Afrika.

Amma yace a farko Afrika ta bari an kwashi albarkatunta a farashi mai rahusa,amma yanzu abin ba haka yake ba tunda China da Afrika suna gudanar da ciniki ne kann farashi dake kasuwannin duniya.

Bayanai daga maaikatar ciniki ta Sin sun nuna cewa,shekarar bara dai kasuwanci tsakanin Sin da Afrika ya kai na dala biliyan 55 da rabi,wanda ya samu karin fiye da kashi 40 cikin dari daga 2005.