1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Sin rage aiwatar da hukuncin kisa

Zainab Mohammed Abubakar
March 12, 2017

Babban alkalin Sin ya ce kasarsa wadda ake cewa ta fi ko wacce aiwatar da hukuncin kisa, ta na zartar da irin wannan hukunci ne a kan mutane kalilan da suka aikata manyan laifuka

https://p.dw.com/p/2Z4BW
Gefängniswärter in Peking China
Hoto: picture-alliance/dpa/D. Azubel

Bayanai kan yawan mutanen da aka aiwatar da hukucin kisa a kansu a kasar ta Sin dai, sirri ne na gwamnati. Sai dai matakin da aka dauka a shekara ta 2007, na cewar dole sai an sake nazarin duk wani hukuncin kisa da kotun kolin kasar ta zartar, ya rage yawan wadanda ake kashewa.

A rahoton da ya gabatarwa sashin shari'ar kasar, babban alkali Zhou Qian ya jaddada cewar, kotuna sun rage yawan mutanen da ake yankewa hukuncin kisa, sai dai bai bada adadin wadanda aka kashe ko kuma ke jiran a zartar da irin wannan hukunci a kansu ba.

Wata kungiyar kare hakkin jama'ar kasar Dui Hua mai matsuguni a Amurka, ta ce a shekara ta 2013 wajen mutane 2,400 aka kashe ta wannan hukunci, kuma adadin bai sauya ba a shekarun 2014 da 2015.