Kasar Sin da Biritaniya sun kulla yarjeniyoyi.. | Labarai | DW | 13.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Sin da Biritaniya sun kulla yarjeniyoyi..

An gudanar da wata tattaunawa ta keke da keke a tsakanin Faraministan Biritaniya ,Mr Tony Blair da takwaran sa na Sin , wato Mr Wen Jiabao.

Tattaunawar da aka gudanar da ita a birnin London, ta tabo batutuwa ne da suka shafi kara kulla dangantaka ta kasuwanci, a tsakanin kasashen biyu.

Ragowar batutuwan da tattaunawar shugabannin biyu ta tabo sun hadar da rikicin yankin gabas ta tsakiya da rikicin nukiliyar kasar Iran da kuma koriya ta arewa.

Bugu da kari Mr Blair da Wen Joaboa, sun kuma tabo batutuwa da suka shafi abubuwan dake faruwa a yankin Darfur na kasar Sudan.

A cewar firimiyan na Sin, Kasar sa ta goyi bayan tura dakarun sojin Mdd izuwa yankin na Darfur, to amma idan mahukuntan Sudan sun amince da hakan.