Kasar Russia zata gayyaci Hamas don tattaunawa | Labarai | DW | 09.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Russia zata gayyaci Hamas don tattaunawa

Shugaba Vladimir Putin na Russia yace zai gayyaci kungiyyar Hamas ta masu kishin addinin Islama izuwa kasar don tattaunawa.

Shugaba Putin ya fadi hakan ne a lokacin wani taron manema labarai a birnin Madrid a yau alhamis din nan.

Wannan dai bayani na Putin da alama ka iya bude kafar cacar baka a tsakanin ta da Amurka, bisa la´akari da matsayin kasar a game da kungiyyar ta Hamas.

Kasar dai ta Amurka tace ba zata yi hulda da kungiyyar ta Hamas ba matukar, bata yarda da kasancewar ci gaba da zaman Israela ba.

Bisa kuwa wannan bayani na Putin, shugaban kungiyyar ta Hamas Isma´il Haniyya yace a shirye kungiyyar take ta amsa wannan gayyata daga mahukuntan na Russia.