1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Rasha ta gargadi Amirka kan Siriya

Mouhamadou Awal Balarabe
April 10, 2018

Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Wassily Nebensja ya bayyana cewar duk wani hari na Amirka a Siriya bisa zargin amfani da makami mai guba zai mayar da hannu agogo baya a kokarin warware rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/2vkgr
USA | UN-Sicherheitsrat - Vertreter Russlands und UK streiten über Fall Skripal
Hoto: Reuters/L. Jackson

Kasar Rasha ta gargadi Amirka dangane da illar da ke tattare da matakin soji da wasu kasashen yammacin duniya ke da niyar dauka a Siriya idan zargin da ake yi wa Bashar al-Assad na amfani da makami mai guba ya tabbata. Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Dubiya Wassily Nebensja ya bayyana yayin taron kwamitin tsaro cewar duk wani hari na Amirka zai mayar da hannu agogo baya a kokarin warware rikicin da ake yi a Siriya.

Sai dai kuma shugaba Trump ya bayana wa manaima labarai cewar ya na shirin yanke shawara kan matakin da zai dauka a kan gwamnatin Bashar al-Assad bayan da ya sake tattauna da shugaban Faransa Emmanuel Macron kan wannan batu, yana mai cewa ba zai lamunta da amfani da makamai masu guba a kan 'yan tawaye ba.

A cewar 'yan gwagwarmaya na kasar Siriya, an kashe mutane fiye da 150 kuma kusan duba sun ji rauni a harin da sojojin Siriya suka kai da guba a garin Duma a ranar Asabar.