Kasar Rasha ta baiyana komawa tura iskar gas zuwa Turai | Labarai | DW | 03.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Rasha ta baiyana komawa tura iskar gas zuwa Turai

Kasar Rasha tace zata koma aikin samarda iskar gas ga kasashen turai,yayinda jamian kasar Ukraine suka garzaya zuwa kasar ta Rasha domin tattauna hanyoyin da zaa kawo karshen wannan takaddama.

A halin da ake ciki kuma,Prime ministan kasar Rasha Mikhail Fradkov,yayi kira ga Kungiyar Taraiyar Turai da ta ,matsawa kasar Ukraine lamba domin ganin an tabbatar da samar da iskar gas zuwa kasashen turai.

An shirya wani taron kungiyar a gobe laraba idan Allah ya kai mu a Brussels,domin tattauna yadda zaa ci gaba da kai iskar gas zuwa kasashen turai cikin wannan takaddama da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine.

Moscow ta zargi Ukraine da satar gas da ake turawa zuwa kasashen turai,wadanda tuni suka fara kokawa da karancin iskar gas,yayinda Ukraine kuma tace Rasha bata bayarda isashen gas da zai wadata kasashen turai.