1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Masar ta kara waadin mayarda yan Sudan gida

January 5, 2006
https://p.dw.com/p/BvDl

Kasar Masar ta amince ta dakatar da batun mayarda yan gudun hijira na Sudan su fiye da 600,wadanda take tsare da su bayan yan sanda sun kawo karshen zanga zanga na yan gudun hijirar a wajen ofishin hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a birnin Alqahira.

Wani kakakin hukumar yace Masar ta amince dakatar da mayarda yan gudun hijirar da kwanaki uku.

Masar ta tsare yan Sudan din fiye da 2000 wadanda suke gudun hijira ko neman mafakar siyasa a lokacin tarzomar da sukayi wadda tayi sanadiyar mutuwar yan Sudan 28,daruruwa kuma suka samu rauni.

A halin yanzu suna tsare a sansanonin soji dake birnin Alqahira.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun nuna damuwarsu game da tsaron wadanda zaa mayar gida.