1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Maroko na ci gaba da gallaza wa makaurata bakaken fata daga yankunan Afirka kudu da Sahara.

YAHAYA AHMEDOctober 14, 2005

Duk da nuna bacin ran da gamayyar kasa da kasa ke yi game da halin da makuarata daga yankunan Afirka bakar fata ke ciki a kasar Marokko, mahukuntan kasar na ci gaba da gallaza musu. Rahotannin baya bayan nan na nuna cewa, har ila yau ba a san makomar kusan `yan bakaken fata dubu daya da aka jibge su a cikin hamadar ba tukuna.

https://p.dw.com/p/BvYm
Wasu daga cikin makaurata bakaken fata da mahukuntan Maroko suka jibge su cikin hamadar Sahara.
Wasu daga cikin makaurata bakaken fata da mahukuntan Maroko suka jibge su cikin hamadar Sahara.Hoto: AP

A kauyen Zoukrane, da ke can cikin hamada, kusa da iyakar Maroko da Aljeriya ne ake zaton sojojin kasar Marokon sun tsare makaurata daga yankunan Afirka bakar fata, su kusan dubu. Da can dai an jibge wadannan makauratan ne cikin hamada, ba ruwa, ba abinci. Bayan kururuwar da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka yi ta yi ne, sojojin kasar suka kwaso wasu daga cikinsu suka tsare su a sansaninsu da ke kauyen na Zoukrane.

Kungiyoyin ba da taimamkon agaji da na kare hakkin dan Adam sun nuna takaicinsu ga yadda mahukuntan kasar Marokkon ke gallaza wa makauratan. Wasu rahotanni sun ce an kai wasu makauratan kuma can cikin hamada a yankin Yammacin Sahara da Marokkon ta mamaye don jibge su a can. A duk wannan yankin kuma, ana zaton cewa, akwai nakiyar karkashin kasa da aka bibbine, wadanda za su iya tashi su halakad da mutane idan sun bi kansu.

Game da wannan halin dai, Hukumar Kula da `Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ita ma ta shiga cikin masu yi wa Marokkon kakkausar suka. Wata kakakin Hukumar ta bukaci jami’an kasar ta Marokko su bayyana wa Majalisar Dinkin Duniya, inda suka jibge sauran makauratan da kuma irin halin da suke ciki. Hukumar da ta kuma ce tana zaton kusan mutane dari 2 da 50 ne a halin yanzu ba a san makomansu a cikin hamadar ba tukuna. Sabili da haka ne dai ta tura jiragen sama masu saukar ungulu zuwa yankunan hamadan don su binciko ko za su ga alamunsu.

Har ila yau dai, babu sahihan alkaluma a kan yawan `yan Afirka bakaken fatan da suka rasa rayukansu. Jami’an kungiyoyin ba da taimakon agaji da likitocin kungiyar nan ta Medecin Sans Frontière da suka yunkuri shiga cikin sansanin sojin na Kauyen Zoukrane, don kai wa mutanen da aka tsaren taimako, sun ce ba su sami damar yin haka ba, saboda sojojin Marokkon sun hana su shiga. Bugu da kari kuma, mahukuntan Marokkon sun ki ba da bayanai game da irin halin da suke suke ciki ko kuma irin matakan da suke niyyar dauka a kansu.

Kungiyoyin sun ce babu kuma tabbas kan makomar maneman mafaka da wasu `yan Afirka bakar fatan da ke zaune bisa ka’ida a Marokkon. Tuni dai an tsare wasu daga cikinsu a kurkuku a garin Taza da ke gabashin Marokkon. Kuma bisa dukkan alamu, mahukuntan kasar na niyyar fid da su gaba daya ne ma daga kasar, duk da cewa suna da cikakkun takardunsu na zama bisa ka’ida. Wasu rahotanni kuma sun ce, an kame wasu jami’an kungiyoyin kare hakkin dan Adam, saboda yunkurin da suka yi na ceto wasu daga cikin `yan bakaken fatar.

A halin yanzu dai, Hukumar Kula da `Yan Gudun Hijira Ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce tana kokarin gano ko mutane nawa ne mahukuntan Marokkon suka kwashe su suka jibge cikin hamada. Hukumar ta yi Allah wadai da irin wannan mugun halin da mahukuntar kasar ke nuna wa makauratan daga yankunan Afirka bakar fata. Har ila yau dai, inji kakakin hukumar, kasar Marokko na nesa da kasancewa kasar dimukradiyya, kuma ba kasa ce mai bin tafarkin shari’a da nuna adalci bisa ka’idojin gamayyar kasa da kasa ba.