Kasar Mali Na Daya Daga Cikin Kasashen Dake Samun Makamashi Daga Haske Rana | Siyasa | DW | 03.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kasar Mali Na Daya Daga Cikin Kasashen Dake Samun Makamashi Daga Haske Rana

Kasar Mali dai kasa ce dake da albarkar rana da iska kuma a sakamakon haka gwamnati ke bakin kokarinta wajen dogara akan zafin hasken rana domin samun wutar lantarki

Taswirar kasar Mali

Taswirar kasar Mali

A taron da ake yi akan sabbin hanyoyin samun makamashi a nan birnin Bonn yanzu haka, kamfanoni da dama kan yi ca kan tawagar wakilan kasar Mali dake halartar taron domin bayyana musu irin ci gaban da suka samu a fasahar aiwatar da karfin hasken rana da na iska. Wadannan sabbin hanyoyin samun makamashi na da muhimmanci ga makomar kasar Mali mai yawan jama’a miliyan 12. Gwamnatin kasar ta himmatu wajen kashe makudan kudi akan fasahar samar da wutar lantarki daga karfin hasken rana. A lokacin da yake bayani game da haka Amadou Tandia, shugaban hukumar kula da al'muran makamashi da wutar lantarki a yankunan karkara ta kasar Mali cewa yayi:

Allah Ya fuwace mana albarkar rana, duka-duka abin da muke bukata shi ne fasahar aiwatar da ita. A halin yanzu haka gwamnati ta fara karya farashin na’ura mai amfani da hasken rana domin yadawa tsakanin jama’a. Tare da taimako daga gwamnati suna iya sayen dukkan kayayyakin akan farashi mai rafusa.

Kasar ta Mali dai ta fi dogara ne akan madatsun ruwa domin samun kashi 70% na wutar lantarki da take bukata. Amma dangane da sauran hanyoyin samun makamashin kasar na fama da koma baya duk da radadin zafin hasken rana da al’umarta ke fama da shi. Duka-duka yawan abin da take aiwatarwa daga wannan bangare bai wuce kashi daya cikin dari ba. To sai dai kuma kamar yadda Amadou Tandia ya nunar, babbar manufar da gwamnati ta sa gaba shi ne na dukufa akan karfin hasken ranar nan gaba. Tun abin da ya kama daga shekarar 1966 ne, wato jim kadan bayan samun ‚yancin kanta, kasar Mali ta fara mayar da hankali akan nagartattun hanyoyin samun makamashi marar illa ga kewayen dan-Adam. Kasar na da kafofi masu yawan gaske dake kula da wannan kasaitaccen buri. Kuma Mali ka iya zama abar koyi ga sauran kasashen Afurka a cewar Andre Toure, sakatare-janar a ma’aikatar makamashi ta kasar. A matsayinta na kasa matashiya Mali na bakin kokarinta wajen dogaro da kanta a fannin makamashi ganin yadda hauhawar farashin mai kan yi mummunan tasiri akan tattalin arzikinta. Bugu da kari kuma tilas ne mutum ya rika sara yana duban bakin gatarinsa dangane da wani takunkumin haramcin sayar da mai da kasar zata iya fuskanta in ji Ibrahim Togola, darektan wata kungiya mai zaman kanta a kasar ta Mali kuma kwararren masani a al’amuran makamashi. Ya ce abin lura a nan shi ne yadda a cikin kiftawa da Bisimillah farashin mai kan yi tashin gwaron zabo, ita kuma Mali kasa ce ‚yar rabbana ka wadata mu. Ta la’akari da haka ya zama wajibi akanta ta mayar da hankali ga fasahar aiwatar da karfin hasken rana, wadda albarka ce da Allah Yayi wa kowa-da-kowa, ba wani mai ikon hana wanzuwarta.