KASAR LIBYA TAYI TASHIN GWAURON ZABI... | Siyasa | DW | 15.01.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

KASAR LIBYA TAYI TASHIN GWAURON ZABI...

A yanzu haka dai kasar Libya ta dukufa kain da nain wajen gudanar da kamfe na samun karbuwa wajen kasashen da suka ci gaba a duniya ta fannoni daban daban na rayuwa,musanmamma kasar Amurka da kuma kasashen nahiyar Turai. A dai yan kwanakin baya da suka wuce,shugaban kasar ta Libya Mohd Ghaddafi yayi ´namijin kokari wajen kara kulla dangantaka a tsakanin kasar tasa da kuma Kasar Amurka a hannu daya kuma da kasashen nahiyar Turai na farko ta hanyar wasti da aniyar da kasar ta dauka a baya na kera makaman nukiliya na biyu kuma kammala biyan kudin diyya ga iyalan wadanda hatsarin jirgin nan na Lockerbie ya rutsa dasu a shekara ta 1988.
Bugu da kari a kuma yan watannin baya kadan da suka wuce kasar ta Libya tasa hannun yarda da biyan kudin diyya ga iyalan wadanda hadarin jirgin nan na Faransa ya rutsa dasu a cikin sahara a shekara ta 1989.
Babban dai abin da yafi burge kasashe na duniya masu fada aji shine sanarwar da kasar ta bayar na watsi da aniyar ta ta kera makaman nukiliya tare da maraba da sifetocin mdd izuwa kasar don gudanar da bincike a kai.
Bisa kuwa ire iren wadan nan namijin kokarin da kasar ta Libya tayi take kuma kann karasa ragowar a halin yanzu,tuni mdd ta bayar da sanarwar dage mata takunkumin data lakaba mata shekara da shekaru.
Bugu da kari a karon farko zauren taron tattalin arziki na duniya da aka shirya yinsa a ranar 21 izuwa 25 na watan nan da muke ciki ya gayyaci kasar ta Libya data halacce shi. Masu shirya wannan taron kolin dai sun nunar da cewa gayyatar kasar ta Libya nada nasaba ne da irin kokarin da takeyi ne wajen gyara huldar dangantakar ta da sauran kasashe da sukaci gaba na duniya.
Abin da dai yanzu ya ragewa kasar shine Amurka ta cire mata takunkumin data saka mata. To amma kuma mahukuntan kasar sunce zasuyi hakan ne kadai idan sun gamsu da irin goyon bayan da mahukuntan kasar Libya ke bawa sifetocin mdd da aka shirya cewa zasu je kasar don gudanar da bincike tare da halaka sauran makaman da kasar suka shirya amfani dasu wajen kera makaman nukiliya.
Bisa hakan nema wasu jamian kasar ta Amurka sukace a yanzu haka suna nan suna tunanin kafa zangon soji a kasar ta Libya don taimakawa sifetocin bincike na kasar da kasar Biritaniya gudanar da aikin nasu.
Shi kuwa faraministan kasar ta Libya Shukri Ghanem cewa yayi a yanzu haka kasar sa ta mayar da hankali ne wajen gyara tare da samar da abubuwan more rayuwa ga yan kasar sakamakon tabarbarewa da sukayi sakamakon takunkumi da aka saka mata na tsawon shekara da shekaru. Faraministan yaci gaba da cewa kasar zata samu galabar yin hakan ne ta hanyar rage sayo makamai masu yawa da kasar takeyi a baya.
A kuwa ta bakin wani malamin jami,a na kasar mai suna Samira Ali cewa yayi shugaban kasar ta Libya ya dauki wadan nan matakan ne ganin cewa idan baiyi hakan ba to babu yadda za,ayi burin sa ya cika na farfado da tattalin arzikin kasar da kuma dinke barakar dake akwaia Nahiyar Africa don samun wanzuwar zaman lafiya da kuma ci gaba.
 • Kwanan wata 15.01.2004
 • Mawallafi Ibrahim sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvmY
 • Kwanan wata 15.01.2004
 • Mawallafi Ibrahim sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvmY