Kasar Libya ta nuna adawa da ahuwa da akyiwa jamian kiwon lafiyan Bulgaria | Labarai | DW | 26.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Libya ta nuna adawa da ahuwa da akyiwa jamian kiwon lafiyan Bulgaria

Kasar Libya ta aike da takardar nuna adawarta game da ahuwa da gwamnatin Bulgaria tayiwa maakatan kula da lafiyan nan 6 na Bulgaria da ake zargi da yiwa yara fiye da 400 allurar kwayar cutar HIV.

Iyalan wadannan yara sunyi Allah wadai da afuwa da akayiwa wadannan nas nas da kuma likita suna masu kira ga gwamnatin Libya data yanke hulda tsakaninta da Bulgaria da korar dukkan yan kasar bulgaria dake Libya gida tare da sake tsare maaikatan na jiyya.

Shugaban kasar Bulgaria Georgi Parvanov ne ya sanarda ahuwa ga wadannan jamian kiwon lafiya 6 yayinda suka isa birnin Sofia.

Takaradar dai tace kasar ta Bulgaria ta karya yarjejeniyar musayar fursunoni ta kasa da kasa,wadda a karkashinta maaikatan jiyyan zasu kammala zamansu na kurkuku a kasar ta Bulgaria.