Kasar Kongo na bukatar tallafi don dasa mulkin dimokradiyya | Labarai | DW | 11.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Kongo na bukatar tallafi don dasa mulkin dimokradiyya

Shugaban kasar Tanzania, Jakaya Kikwette yace kungiyyar raya kasashen kudancin Africa, nada babban kalubale na ganin cewa ta tallafawa kasar Kongo kama turbar mulki irin na dimokradiyya.

Mr Kikwette , wanda ya fadi hakan a babban birnin kasar Namibia, wato Windhoek, yaci gaba da cewa kungiyyar su ta SADC zata sauke nauyin dake kann nata ne ta hanyar tallafawa kasar da abubuwan daya kamata , a lokacin zaben gama gari da aka shirya yi a nan gaba.

Rashin ingantattaun hukumomi da zasu aiwatar da matakan gwamnati a kasar a cewar Mr Jakaya, na daga cikin dalilan daya ke kara mayar da kasar ta Kongo baya.

Bisa hakan, shugaban na Tanzania ya tabbatar da cewa ya zama wajibi, kungiyyar SADC ta tabbatar da cewa zaben na Kongo ya gudana a cikin tsafta da kwanciyar hankali, don saisaita linzamin mulkin dimokradiyyar da ake shirin kafawa a kasar.

A yanzu haka dai kasar ta Namibia ce ke rike da shugabancin ragamar kungiyyar ta SADC, a inda kasar ta Tanzania ke a matsayin mataimakiya.

Rahotanni dai sun nunar da cewa shugaban kasar na Tanzania dai na kasar ta Namibia ne aci gaba da ziyarar aiki ta kwanaki uku da yake a kasar.