1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Jamus ta baiyana takaici da rasuwar sojin ta a kasar Afghanistan.

Mai rikon mukamin ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer yace gwamnatin kasar Jamus ta kadu matuka da kashe sojin ta guda tare kuma da wasu mutane biyar yan Afghanistan a wani harin kunar bakin wake a birnin Kabul. Yana mai cewa harin ya nuna har yanzu akwai sauran rina a kaba a kokarin da ake na tabbatar da cikakken tsaro da kwanciyar hankali a Afghanistan. A ranar Litinin ne dai wani dan kunar bakin wake dauke da nakiyoyi a cikin motar sa ya afkawa motar dake dauke da dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar tsaro ta NATO wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojin daya da jikata wasu sojojin guda biyu. Mayakan sa kai na kungiyar Taliban sun baiyana cewa sune ke da alhakin kai wannan harin.