1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Italiya ta shiga rudani na siyasa

Yusuf Bala Nayaya MNA
May 28, 2018

Kasar Italiya ta tsinci kai a yanayi na rudanin siyasa bayan da yunkurin masu adawa da baki ya ci tura na kafa gwamnati, inda tuni shugaban kasar ya nemi wanda zai jagoranci gwamnati gabanin sake zabe.

https://p.dw.com/p/2yQp2
Italien Regierungsbildung gescheitert - Präsident Mattarella
Shugaba Sergio Mattarella na ItaliyaHoto: Reuters/A. Bianchi

Shugaba Sergio Mattarella ya yi amfani da karfin ikonsa wajen hana dan gaba-gaba Turai sai 'ya'yanta wato Paolo Savona don ya zama ministan tattalin arzikin Italiya, lamarin da ya sanya wanda 'yan jam'iyyar Five Star Movement da masu adawa da baki suka zaba a matsayin firaminista Giuseppe Conte, ya ce ya ajiye nauyin kafa gwamnati da aka dora masa a makon jiya.

Shugaba  Mattarella na Italiya dai ya ce zai amince da kowane minista da 'yan adawar suka gabatar masa amma ban da Savona wanda ya kira kudin bai daya na Euro a matsayin wani "keji na Jamus" wanda kuma ya kudiri aniya ta ganin Italiya ta fice daga tsarin amfani da kudin na bai daya "idan bukatar hakan ta taso."