Kasar Isra’ila ta ce a shirye take da janye kawanyar da take wa gabar tekun kasar Lebanon a cikin sa’o’i 48 masu zuwa | Labarai | DW | 08.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Isra’ila ta ce a shirye take da janye kawanyar da take wa gabar tekun kasar Lebanon a cikin sa’o’i 48 masu zuwa

Israila tab a da sanar cewar a shirye take ta dakatar da kawanyar da take wa gabar tekun kasar Lebanon cikin awa 48, bayan ta gamsu da alkawarin MDD mai cewar zata tsugunar da sojojin ta na kasa da kasa domin hana sufurin makamai ga dakarun Hizbullah. Kasashen Faransa, Italiya da Girka sun yi alkawarin bada jiragen ruwa ga rundunar wadanda zasu rika santiri a gabar tekun Lebanon har tsawon makonni uku lokacin da rundunar sojin ruwa ta kasar Jamus zata karbi aikin. Daman ana ta kai ruwa rana a nan Jamus akann tsayar da lokaci da kuma irin dokokin da rundunar sojin zata yi aiki dasu. Ranar alhamis ne Israila ta dakatar da matakinta na toshe hanyoyin jiragen sama na Lebanon wanda ta fara lokacinda ta kaiwa kasar hari a watan juli da ya gabata.