KASAR IRAQI A YAMMCIN YAU LITININ. | Siyasa | DW | 16.08.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

KASAR IRAQI A YAMMCIN YAU LITININ.

Kamar yadda kamfanin dillancin labaru na AFP ya bayyana,wakilan da gwamnatin iraq mai rikon kwarya ta nada,wadanda zasu kai ziyara garin najaf don tattaunawar sulhu da shugaban shiawa Muqtadr Sadr,sun fasa wannan ziyara a yammacin yau kamar yadda aka shirya da fari.

Bayan da mai magana da yawun shiawan ya bayyana cewa a shirye suke dasu hau teburin sulhu da wadannan wakilai na gwamnati,sai kuma gashi su wakilan sun fasa kai wannan ziyara har sai safiyar gobe talata kamar dai yadda rahotannin suka bayyana.

A yanzu haka dai a can garin najaf,daruruwan magoya bayan Muqtadr Sadr sun firfito bakin babban masallacin su inda suke gudanar da wata zanga zangar lumana don nuna rashin jin dadin su kann yadda sojin amurkawan tare da goyon bayan sojin iraqi ke ta yakar shiawa a kasar.

Wadannan magoya bayan darikar shiawa,suna dauke ne da hotunan shugaban nasu Muqtadr Sadr,suna kuma rera wakoki na suka ga prime ministan kasar mai rikon kwarya Iyad Allawi tare da gwamnatinsa,a hannu daya kuma tare da yin suka ga dukkan amurkawan dake cikin kasar su.

A yammacin yau ne kuma wani bomb ya tashi a kusa da wani ofishin yan sanda wanda baiyi sanadiyyar rasa rai ko kuma raunana wani ba.sai dai a can maboyar shiawan mutane takwas ne suka samu raunuka sakamakon musayar harsasahi da ake tayi tsakanin su da sojin amurka.

Mahukuntan kasar iraqi,sun bayyana amincewarsu ga bukatar prime minista Iyad Allawi,da yayi kira ga shiawan dasu ajiye makamansu,yin hakan kamar yadda suka amince shine hanya mafi sauki da zaa kawo karshen wannan rikici.

Shi kuwa Fadel Al-khursan,wani dan shia daya halarci wannan babban taro na birnin bagadaza,cewa yayi,yin kira ga shiawa dasu ajiye makaman su ba shine mafita ba,illa kawai a samu tattaunawa dasu don jin bukatarsu.

Idan har aka tattauna babu shakka zaa cimma wata yarjejeniya da zata zamo alheri ga gwamnatin tare da su kansu shiawan.a cewar Sheik Fadel.tunda dai har shiawan sun amince da hawa teburin sulhu.

A wajen wannan taron ne mahukuntan kasar suka shaidawa sheik Fadel cewa bukatarsu itace shiawan su bar wannan masallaci da suke a boye,kuma gwamnati a shirye take ta sama musu wani wurin da zasu iya zama a cikin wannan gari,har ma su basu tabbacin babbu wani mai kai musu hari idan har sun ajiye makamansu kuma sun mika wuya.

A hannu guda kuma kakakin Muqtadr Sadr,Sheik Ahmed Shaibani,ya mai da martani ne da jaddada jawabin sa na cewa a shirye suke da su tattauna da wadannan wakilai na gwamnati don kawo karshen wannan rikici,sai dai kuma ya cigaba da cewa idan har ba wata kyakkyawar yarjejeniya aka cimma ba to fa a shirye suke dasu cigaba da yakar makiyan nasu har sai karfin su ya kare ko kuma sun rasa rayukan su baki daya.

Ana dai sa ran a safiyar gobe talata wadannan wakilai kusan hamsin da gwamnatin kasar ta nada zasu isa garin na najaf don gudanar da wannan tattaunawa da shiawan,wadda ake fatan itace zata kawo karshen wannan rikici daya haifar da mutuwar daruruwan mutane a kasar ta iraqi.

 • Kwanan wata 16.08.2004
 • Mawallafi Maryam L.Dalhatu.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvhH
 • Kwanan wata 16.08.2004
 • Mawallafi Maryam L.Dalhatu.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvhH