Kasar Indiya tana bikin cikar shekaru 60 da samun yancin kanta | Labarai | DW | 15.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Indiya tana bikin cikar shekaru 60 da samun yancin kanta

Firaministan kasar Indiya Manmohan Singh yayi alkawarin bada dala biliyan 6 don bunkasa harkokin noma a kasar a yayinda yake kaddamar da bikin cikar shekaru 60 da samun yancin kasar.Cikin wani jawabi da yayi Singh yace manoma sune kashin bayan kasar.Aana dai gudanar da bikin samun yancin cikin tsauraran matakan tsaro,inda aka jibge dubban jamian tsaron a sassa dabam dabam na kasar bayan samun barazana daga yan kungiyar Alqeda da yan aware na kasar.A jiya talata kasar Pakistan tayi nata bikin na samun yanci tare da yin adduoi na tunawa da dubban wadanda aka kashe a lokacinda suke hijira zuwa Pakistan din a 1947.