1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Faransa ta baiyana kudurin komitin sulhu dake goyon bayan Shawarar AU akan Ivory Coast

Hauwa Abubakar AjejeOctober 14, 2005

Kungiyar AU ta bukaci komitin sulhu ya mara mata baya a kokarin da takeyi na kare barkewar balai a kasar Ivory Coast da ta rarrabe.

https://p.dw.com/p/BvYl
Laurent Gbagbo
Laurent GbagboHoto: AP

Shawarar da kungiyar Taraiyar Afrika ta yanke a ranar 6 ga watan oktoba a birnin Addis Ababa,yayi kira ga shugaba mai ci yanzu Laurent Gbagbo,da ya ci gaba da rike akalar mulkin kasar na Karin shekara guda,bayan karewar waadin ranar 30 ga watan oktoba da muke ciki na zaben shugaban kasa da dukkan bagarori suka amince ba zaa iya gudanarwa ba.

Saboda ta karfafawa yan tawaye gwiwa,tare da damawa da su,kumgiyar ta AU,tayi kira da a nada sabon Prime Minista da zai shugabanci gwamnatin kasar,wadda kuma zai samu karbuwa ga dukkan bangarorin kasar,har sai lokacinda zaa iya gudanar da zabe nan gaba.

Prime minista mai ci yanzu,dan kasuwa Seydou Diarra,yana a bayan fage tun lokacinda aka nada shi karakashin yarjejeniyar zaman lafiya da Faransa ta jagoranta a 2003,amma masu lura da alamura sunce,hakan ba zai rasa nasaba da rashin bashi cikakken iko da shugaba Gbagbo yayi ba,tun bayan nada shin.

A jiya alhamis ne,ministan harkokin wajen Nijeriya,Oluyemi Adeniji,ya baiyanawa majalisar cewa,lokaci sai karatowa yake yi na ranar 30 ga watan oktoba,kuma har yanzu akwai sauran matakai da ya kamata a dauka,yana mai bukatar majalisar ta gaggauta amincewa da shawarar da kungiyar AU ta mika.

Amincewar Majalisar zai baiwa shugaba Najeriya kuma shugaban kungiyar ta AU,chief Olusegun Obasanjo da Shuagaba Thabo Mbeki na Afrika ta kudu,damar kai ziyara zuwa kasar Ivory Coast a karshen wannan mako, a kokarin da sukeyi na ganin bangarorin kasar sun amince da wannan shawarar.

Tun ma kafin majalisar ta gana,shugaban yan tawaye,Guilaume Soro, a jiya alhamis ya jaddada bukatarsa cewa,kada a amincewa shuagab Gbagbo taka wata muhimmiyar rawa cikin gwamnati har zuwa lokacin zabe na gaba.

Yace yana fata komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya,zai amince cewa waadin mulkin Gabgbo ya kare,ya kuma karfafa masa gwiwar ganin yayi ta maza,ya sauka daga mulkinsa.

Amma jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya da Kofi Annan ya nada domin taiamaka shirya zabe a kasar,Antonio Monteiro,ya baiayana fatar cewa,yan tawayen zasu rattaba hannu akan shawarar ta kungiyar AU,da zummar ganin an gaggauta zaben sabon shugaban kasa a kasar ta Ivory Coast.

Antonio ya baiyanawa manema labarai cewa,yanzu ganin zaa rantsar da membobin sabuwar hukumar zabe a ranar litinin mai zuwa,tare kuma da samun hadin kan yan tawaye,zasu tabbatar da shirya zabe cikin dan kankanin lokaci da ba zai wuce watanni shida masu zuwa ba.

Kungiyar AU a halin yanzu tayi kira da a kara karfin yawan dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Ivory Coast,wadanda a halin yanzu suke fiye da 6,600,ciki har da yan sanda na kasa da kasa.