Kasar Eritiriya ta yi tir da harin Habasha
June 13, 2016Talla
Gwamnatin Kasar Eritiriya ta soki lamarin makwabciyarta Habasha kan kaddamar da hari a kan iyakarta. Mazauna yankin da ke kan iyakar kasashen biyu sun shaida wa kamfanin dillancin labaru na Reuters cewar sun ta jin harbe-harben bindigogi tun a ranar Lahadi har zuwa Litinin. Wasu shaidu sun kuma bayyana cewar sun ga dakarun kasar Habasha na kutsa kai i zuwa yankin na Eritiriya.
Kawo yanzu dai, babu wani martani daga bangaren gwamnatin kasar ta Habasha a kan wannan takaddamar, to sai dai daman akwai takun saka tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna wanda yayi sanadiyar salwantar rayuka da dama a shekarun 1998 i zuwa 2000.