Kasar Denmark ta janye jamián jakadancin ta daga Indonesia | Labarai | DW | 13.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Denmark ta janye jamián jakadancin ta daga Indonesia

Gwamnatin kasar Indonesia ta baiyana rashin jin dadi da matakin kasar Denmark na jamián jakadancin ta daga birnin Jakarta a sakamakon zanga zangar data biyo bayan batancin da Jaridar Denmark ta yi ga Manzo Annabi Muhammad S.A.W. Gwamnatin Denmark din ta kuma bukaci daukacin yan kasar ta dake zaune a Indonesia da su gagauta ficewa daga kasar domin kare lafiyar su bisa abin da ta baiyana da cewa barazana da ake musu. Tun dai Denmark din ta janye jakadun ta daga kasashen Syria da kuma Iran.