Kasar belarus ta tabbatar da mutuwar jamianta a Somalia | Labarai | DW | 24.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar belarus ta tabbatar da mutuwar jamianta a Somalia

Kasar Belarus ta tabbatar mutuwar jamianta 11 cikin jirgin saman nan da aka kakkabo jiya a kasar somalia.

Jirgin dai yana kann hanyarsa ce ta dawowa daga kai abinci ga dakarun kasar Uganda dake birnin Mogadishu.

Ministan harkokin cikin gida na gwamnatin wucin gadin ta Somalia Muhammad Mahmud Guled yace an kaddamar da bincike kann musabbabin wannan hadari.

Ministan yace akwai alamun cewa wasu matsaloli na inji suka haddasa wannan hadari,sai dai kuma wadanda suka ganewa idanunsu sunce sun ga lokacinda makami mai linzami ya kakkabao jirgin jim kadan bayan tashinsa daga filin jirgin saman birnin Mogadishu.