1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasafin kuɗin Jamus

March 19, 2010

Majalisar Bundestag ta amince da kasafin kuɗi.

https://p.dw.com/p/MXw3
Majalisar BundestagHoto: AP

Majalisar Dokokin Jamus Bundestag ta amince da kasafin kuɗin baɗi wanda shine mafi yawa a tarihin ƙasar na zunzurutun kuɗi har euro miliyan dubu 320 tare kuma da cin bashin wasu euro miliyan dubu 80. A jawabin sa Ministan kuɗin Jamus Wolfgang Schäuble yace ana buƙatar kuɗin ne domin magance matsalar tattalin arzikin kuɗi na duniya dake addabar al'umman ƙasar. Koda yake ministan yace babu wani shirin gwamnati a yanzu na ƙara yawan haraji, amma kuma shugabar gwamnati Angela Merkel tace za'a ɗauki matakan tsuke bakin aljihun gwamnati. 'Yan majalisa 313 suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da kasafin kuɗin saɓanin 256 da suka ƙi amincewa dashi. A waje ɗaya kuma Gwamnatin Jamus ta shawarci ƙasar Girka dake fama da matsalar kuɗi data tuntuɓi hukumar bada lamani ta duniya IMF domin samun tallafi. Kakakin gwamnatin yace Jamus bata ciyanke ƙaunar ganin Girka ta nemi tallafi daga hukumar ta IMF ba, muddin dai duk ƙoƙarin da ƙasshen Turai keyi na tallafa mata yaci tura. Wannan shawara da Jamus ta bayar ana ganin alamu ne dake nuna sabon matakin ƙasar na dawowa rakiyar ƙasar ta Girkan wajen samun tallafi daga hukumar ta IMF.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Halima Balaraba Abbas