Kasa ta kara girgiza a Pakistan | Labarai | DW | 19.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasa ta kara girgiza a Pakistan

A Pakistan kasashe da kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa na ci gaba da kai tallafi da milliyoyin al´umomin da girgizar kasa ta rutsa da su, a makon da ya gabata.

A na cikin wannan mayuyacin halin wata sabuwar girgizar kasar ta abku sahiyar yau a arewancin kasar ta Pakistan, saidai ba ta hadasa mutuwar rayuka ba, duk kuwa da karfin da ta ke dauke da shi.

A wani mataki na ba zata shugaba Pervez Musharaf na Pakistan, ya bayana bukatar balle iyakoki, tsakanin Pakistan da India, domin baiwa al´ummomin kasashen 2, da ke yankin Kashemir, damar tsalakawa sun binciki gawwarwakin dangin su, da girgizar kasar ta rutsa da su.

Hukumomi India, sun yi lale marhabin da wannan mataki, saidai babu cikaken bayani a game da ranar da zai fara aiki a zahiri.