1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karzai yace ya gana da yan Taliban

April 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuO8

Shugaban lkasar afghanistan Hamid karzai yace ya gana da wasu yan kungiyar taliban a kokarinsa na sansanta rikicin kasar.

Karzai yace bayan ganawara komitin Taliban dana gwamanai,shi kansa ya gana da wakilan taliban amma banda Mullah Omar.

A wani labarin kuma wani dan kunar bakin wake ya kashe akalla mutane 5 a birnin kabul na kasar Afghansitan.

Yan sanda sunce mutumin yana zaune ne cikin motarsa a wajen majalisar dokokin kasar a lokacinda ya dana bam din yayinda wasu yan sanda suka nufi inda yake.

A kudancin kasar kuma,yan kungiyar Taliban sun kame lardin Khak Afghan,inda yan sanda suka janye a lokacinda yan taliban din suka kaiwa yankin hari.

Wannan kuwa ya faru ne a lokacinda yan sanda suke ci gaba da neman wasu maaikatan agaji 2 yan kasar Faransa da wasu yan kasar ta Afghanistan su 3 wadanda yan taliban sukayi garkuwa da su tun ranar talata.