1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kananan yara na ci gaba da neman mafaka a Turai

Lateefa Mustapha Ja'afarMay 2, 2016

Kimanin yara da ke da kananan shekaru 90,000 ne suka shigo kasashen Turai a shekara ta 2015 ba tare da wani makusancinsu ba domin neman mafaka.

https://p.dw.com/p/1IgmA
Yara masu kananan shekaru na neman mafaka a Turai
Yara masu kananan shekaru na neman mafaka a TuraiHoto: picture alliance/dpa/S. Suna

Wani kiyasi da wata hukumar kididdiga ta kungiyar Tarayyar Turai wato EU ta gudanar, ya nunar da cewa adadin nasu dai ya ninka har sau hudu idan aka kawatanta da masu karancin shekarun da suka shigo Turai domin neman mafaka daga shekara ta 2008 zuwa 2013. Rahotanni sun nunar da cewa daga cikin yaran da shekarunsu suka kama tsakanin 16 zuwa 17 su 88,300 wadanda kaso 91 cikin 100 suka kasance yara maza da suka nemi mafakar a kasashen Turai, kaso 51 sun fito ne daga kasar Afghanistan. Kawo yanzu dai kasar Sweden ta yi wa yaran da basu da wani makusanci da ke neman mafakar a Turai su 35,300 rijista, yayin da Jamus ta karbi bakuncin 14,400 yayin da sauran suka samu rijista a kasashen Hangarai da Ostiriya.