Karuwar mutuwar mata da yara a nahiyar Afrika | Labarai | DW | 20.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karuwar mutuwar mata da yara a nahiyar Afrika

Kungiyar kula da Lafiya ta Mdd WHO ta bayyana cewa millioyoyin iyaye mata da yara kanana ne ke mutuwa daga cututtuka da zaa iya karesu ,duk da alkawura ingantacciyar hanyar kula da lafiya da gwamnatoci da kasashen dake bada agaji keyi.Sakamakon annobar cutar Aids da rigingimu na fada,harkokin kula da lafiya na kasashe da dama nacigaba da kasancewa cikin halin rashin tabbas,ayayinda a wasu kasashen lamuran na dada tabarbarewa.Kungiyar ta WHO ta bayyana cewa daga cikin kasashe 20 da akafi samun yawan mace macen iyaye mata,19 na daga nahiyasr Afrika.Kazalika an bayyana cewa Afrika ce keda mafi yawan yara kanana dake mutuwa a fadin duniya baki daya.Matsalar cutar Malaria na cigaba da yin barazana wa rayuwan kananan yaran da shekarunsu basu shige biyar da haihuwa ba.Adangane da hakane kungiyar ta yi kira ga gwamnatocin kasashen dasu tashe tsaye wajen inganta harkokin lafiyan alummom,insu musamman mata da yara.