1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar hare-hare kafin zaben Afghanistan

Yusuf Bala Nayaya
May 6, 2018

Akalla mutane 30 ne suka samu raunika wasu sun mutu bayan tashin bam a wata cibiyar rijistar masu zabe a gabashin Afghanistan lamarin da jami'ai suka ce ya kawo rufa mako da kwararar da jinin al'umma.

https://p.dw.com/p/2xFyv
Afghanistan Kabul Doppelanschlag
Hoto: Reuters/O. Sobhani

Mutanen dai da lamarin ya ritsa da su sun fito ne daga masallaci a kokari na yin rijista a cibiyar da ke a gaban masallacin sai bam ya tashi da su. Gul Mohammad Mangal da ke zama jami'in kula da lafiya a lardin na Khost ya ce mutane 12 ne suka mutu 33 kuma suka samu raunika, sai dai ya ce adadin zai iya karuwa kasancewar wasu marasa lafiyar yanayin nasu ya munana.

Wannan hari dai na zuwa mako gabannin zabe wanda ma kafin shi an kai wasu hare-haren da suka yi sanadi na rayukan mutane 25 a birnin Kabul. Akwai kuma wasu tara da suka mutu ciki har da me daukar wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP hotuna Shah Marai. Shi kuwa Ahmad Shah mai aika rahoto ga BBC a wani harin ne aka halaka shi a lardin na Khost.