Karuwar bakin haure bisa hanyar tekun Bahar Rum | Labarai | DW | 26.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karuwar bakin haure bisa hanyar tekun Bahar Rum

Daruruwan 'yan gudun hijira ne aka ceto a yankin ruwan Libiya, a cewar kungiyoyin SOS Méditerranée da kuma Médecins sans Frontières da ke bayar da agaji ga 'yan gudun hijira.

Italien Rettung von Flüchtlingen aus dem Mittelmeer vor Sizilien (picture-alliance/Ropi)

'Yan gudun hijra masu zuwa Turai ta tekun Bahrum

Daga cikin mutane kusan dubu daya, an ceto 645 bisa wani jirgin ruwa mai tayoyi, wasu kuma bisa kwale-kwale na itace, bayan da masu ayyukan ceto suka shafe tsawon awoyi shida suna ceton a cewar kungiyar SOS Méditerranée ta shafinta na Twitter. An samu mace daya da ta mutu kafin zuwan masu aikin ceton. A 'yan watannin baya-bayan nan dai ana ta samu karuwar 'yan gudun hijira da ke tashi daga gabar ruwan Libiya zuwa Turai, inda aka samu ceto fiye da mutun dubu shida cikin mako daya, abun da ya kai adadin 'yan gudun hijiran da aka ceto ya zuwa dubu 22 tun daga farkon wannan shekara ta 2017.