1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karshen ziyarar Paparoma a London

Paparoma Benedict na 16 ya kammala ziyararsa mai cike da tarihi a London.

default

Paparoma Benedict a lokacin ziyararsa a Birmingham,

Paparoma Benedict na 16 ya kammala ziyarar yini hudu da ya kai Britaniya tare da jagorantar tsarkake wani masanin addinin addinin Kirista na karni na 19 Cardinal John Newman a Birmingham. Newman ya kasance daga cikin yan kungiyar Oxford wadanda suka dabbaka yunkurin sanya daib'un darikar Katolika a cikin tsarin mujai'ar Anglican. A ranar Asabar da ta wuce sai da Paparoman ya gana da wasu mutane biyar wadanda manyan limaman cochi suka yi lalata da su a lokacin da suke kananan yara. Paparoman ya baiyana matukar takaicinsa dangane da wannan danyen aiki wanda ya baiyana da cewa babban abin kunya ne ga cochin katolika baki daya. A waje guda kuma dubban jama'a sun gudanar da zanga zanga domin nuna bacin rai da yadda Paparoman ya tafiyar da batun tabargazar lalatar da kananan yaran.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Umaru Aliyu