Karshen ziyarar Horst Koehler a Uganda | Zamantakewa | DW | 06.02.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Karshen ziyarar Horst Koehler a Uganda

Ziyarar Shugaban Jamus a yankin arewacin Uganda

default

Shugaban Ƙasar Jamus, Horst Koehler da Uwargidan sa Eva a arewacin Uganda.

A ranar karshe ta rangadinsa na ƙasar Uganda, shugaban Jamus Horst Khöler ya ziyarci arewacin Uganda, inda ya gana da daruruwan mutane musanman yara don jin yadda suke farfadowa da bala'in yaki na tsawon shekaru 20.

Na kawo wannan ziyarar ne don in tabbatarwa al'uman arewacin Uganda wadanda ke cikin mawuyacin hali cewar ba mu manta dasu ba, kuma muna tare dasu a halin da suke ciki. Muna sane da irin wahalolin da suke fuskanta wanɗanda bamu iya kwatantawa tun fiye da shekaru 10 da suka gabata, amma ina tabbatar musu cewar muna tare dasu, kuma bazamu taba mancewa dasu ba. Kuma inason su san cewar bayan Uganda akwai wasu kasashen duniya da ke damuwa da halin da suke ciki.

A daya daga wuraren da aka yiwa dubban al'uman arewacin Uganda da suka rasa gidajensu masauki sakamakon shekarun yake-yake da ƙungiyar 'yan tawayen kasar da aka fi sani da LRA, watau Coo Pe Tun, shugaba Köhler ya yaba da ayyukan da Ƙungiyoyin agaje ta ƙasa da ƙasa, kamarsu World Vision da Ƙungiyar Red Cross, ke yi na taimakawa fiye da 'yan gudun hijira miliyan daya da digo bakwai. Shugaban ya gana da wasu 'yan gudun hijira da ke samun kula a harabar Coo Pe Tun, wadanda suka bayyana masa cewar har yanzu suna cikin zaman dar-dar sabili da yadda 'yan tawayen ke kai musu hare haren ba zato ada, duk kuwa da cewar an fara tattauna batun dauke wuta a yankin tun shekaru biyu da suka gabata.

Yaƙin basasar arewacin Uganda ya taɓarɓare al'amuran gona da kuma sauran harkokin rayuwa na al'uman Acholi da ke arewacin Uganda, inda a yau basu iya nomawa kansu abinci sai dai kawa su dokara kan taimako daga kungiyoyi, gwamnati da kasashen ketare, duk da haka shugaba Horst Köhhler ya ce ya lura mutanen yankin sun gaji da zaman kashe wando da suke ciki.

Wani abin da ke bada kwarin gwiwa a nan shine mutanen na da cikakken shiri kuma sun nuna sha'awa na komawa kauyukansu, don sake shiga harkokin yau da kullu, matasa na sha'awan karatu kana da yawa daga cikin su sun bayyana niyar kama ayyukan yi idan hakan na samuwa.

A yanzu hakan ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta taimaka da kuɗi domin kafa sashen bincike a jami'ar ƙasar da ke Gulu, don masu fama da matsalar gigin barci sabili da yakin basasar ya haifar da munanan matsaloli ga jama'an arewacin Uganda inda ake fama da shaye-shayen giya da sauran abubuwa masu sa maye har ma da kashe-kashe.

A karshe dai shugaba Köhler ya yi kira ga dukkan ɓangarorin da ke gaba da juna a kasar Kenya makwabciyar Uganada da su yiwa Allah su yiwa ma'aiki su koma kan teburin shawara domin shawo kan rikicin kasar a siyasance.