Karshen ziyarar Blair a yankin gabas ta tsakiya | Siyasa | DW | 20.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Karshen ziyarar Blair a yankin gabas ta tsakiya

Tony Blair da Mahmoud Abbas

Tony Blair da Mahmoud Abbas

Prime minista Tony Blair na Britania,yayi kira ga shugabannin kasashen duniya dasu fito fili domin taimawakawa masu tsattsauran raayi dake kasar Iran da sauran kasashe,domin tallafawa samar da zaman lafiya tsakanin Izraela da yankin Palasdinawa.

Mr Blair wanda yake kan kafarsa ta karshe a rangadin aiki daya kai yankin gabas ta tsakiya ,ya bayyana cewa Iran a bayyana tana marawa harkokin taddancin kasar Iraki baya,da yiwa gwammnatin kasar Lebanon kallon hadarin kaji,tare da haifar da karan tsaye a dangane da kokarin samar da zaman lafiya tsakanin izraela da palasdinu.

Iran dai bata taba laakari da Izraela a matsayin yantaciyyar kasa ba,kuma a bara ne shugaba Mahmoud Ahmadinejad yayi kira da a goge,Izraelan daga taswirar duniya.

Iran wadda ke karkashin matsin lamba daga kasashen turai a dangane da shirin nuclearnta ,na marawa kungiyar yan Hizbollahi na kasar Lebanon baya,jammiyar dake tursasa batun gudanar da zabe da wuri ,bayan gaza samun matsayin madafan iko da take nema a gwammantin kasar.Adangane barazanar takunkumi da ake shirin kakabawa kasarsa kuwa Shugaba Ahmedinejad cewa yayi.....”Suna barazanar kakaba mana takunkumi,amma dole ne susan cewa mallakar makamashin wuta na nuklear muradin Iraniyawa ne,kuma a kullum mutane zasu cigaba da matsin lamba adangane da neman yancin su”

Tony Blair wanda zai sauka daga karagar mulki acikin shekaran da zamu shiga,mutumin da kuma taurarinsa suka dusashe sakamakon yakin kasar Iraki,yayi watsi da da maganganun da akeyi nacewa Britania da Amurka ne ke dada ruruta wutan rikicin taaddanci a yankin gabas ta tsakiya.

Ya fadaw taron yan kasuwa a birnin Dubai cewa,lokaci yayi da zaa dakatar da zargin juna,domin idan tasari da manufofin mu suka samu kura kurai,mukan ji kunyan fitowa fili domin bayyana hakan domin kawo sauyi.

Adangane da hakane Mr Blair yayi kira ga shugabanin kasashen yankin gabas ta tsakiya masu sassaucin raayidasu hada karfi da karfe wajen tabbatar da democradiyya,kana da yakar ayyukan tarzoma a daya hannun.

Yace ya zamanto wajibi mu kalubalanci gwamnatin Iran ,wadda ke barazana wa wadannan manufofi namu, a wannan yankin,wanda ke bukatar hadin kan shugabannin.Ziyara ta Blair a yankin gabas ta tsakiya takaishi Turkiyya da Masar da Iraki da Israela da yankin Palasdinawa,kana ya karasa da hadaddiyar daular larabawa.