Karshen taron tsaro a birnin Munich | Siyasa | DW | 12.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Karshen taron tsaro a birnin Munich

An kammala taron kasa da kasa a kan tsaro

Shugaban Rasha Vladimir Putin

Shugaban Rasha Vladimir Putin

Jawabin shugaba Vladimir Putin na Rasha a taron karfafa matakan tsaro na kasa da kasa da aka kammala birnin Munich dake nan tarayyar jamus,na zargin Amurka da ruruwa wutan rikicin karuwan fasahun sabbin makamai a bangaren kasashe da basu da karfi,ya samu martanin ministan tsaron kasar Amurka Roberts Gates da kakkausar Murya.

Mahalarta taron dai sun tabka mahawara a dangane da irin muhimmaiyar rawa da kungiyar tsaro ta arewacin atlantika watau NATO ke takawa wajen tabbatar da tsaro a sassa daban daban na duniya.Akasarin wakilan da suka halarci taron na birnin Munich,sun fito ne daga kasashen dake kungiyar ta NATO,wadanda suka tattauna makomar wannan kungiyar.

Jawabin da shugaban Rasha yayi a ranar asabar a gaban wakilan dake halartan wannan taro dai yayi matukar tasiri.Jawaban Shugaba Vladimir Putin dake zama na farkon irinsa a wurin wannan taro,ya nunar dacewa baya laakari da batutuwan diplomasiyya da ake zayyanawa ba tare da aiwatar dasu ba.

Ya nunar dacewa idan akayi laakari da ayyukan dakarun tsaro na kungiyar Nato,da matsayin Amurka,zaa ga cewa babu wani rawa da ita Amurkan ke takawa wajen kokarin samarda zaman lafiya,bisa laakari da naurorin kare makamai masu linzaminta dake gabashin turai ,da kuma yadda manufofin siyasarta na ketare suke.

Kusan dukkan mahalarta wannan taro daga birnin Moscow dai sunyi nuni dacewa,a yanzu haka duniya ta fara shiga yanayin da kasashe ke ,kokarin mallakin makamai da zasu kare kansu daga barazanar manyan kasashe masu makamai na kare dangi da suka hadar da Amurka,sai dai sun nanata cewa matakan da shugaba Putin ke dauka a kann Tschetscheni,matakai ne da suke bisa hanya madaidaiciya.

Wannan taro na kasa da kasa akan matakan tsaro dai ya tunatar da ababn da suka faru shekaru 60 da suka gabata na yake yake,bisa ga laakari da halin da duniya take ciki a halin yanzu.

Sai dai taron ya jaddada bukatar hadin kai wajen samarda nagartacciyar zaman lafiya a duniya,a maimakon rarrabuwar kawuna da fuskanta a halin yanzu tsakanin nahiyar turai da wasu nahiyoyin.

Batu daya girgiza wannan taron taron da shine irin kalamai na zargin Amurka da shugaban na Rasha ya furta,nacewa manufofinta na soji basa haifar da komai face dada lalata lamura na zaman lafiya,inda ya bada misali da halin da kasar Iraki ke ciki a halin yanzu da dakrun sojin Amurkan ke cigaba dayin kaka gida.Wannan suka da shugaban na Rasha yayi dangane da matakan tsaro dai,ba wani sabon batu bane a tarihin wannan takaddama.

Shekaru 15 kenan bangarorin nbiyu na ganawa sau biyu a kowace shekara domin tattaunawa,sai dai bisa dukkan alamu babu wani tudun dafawa da akan cimma a ire iren wannan tattaunawa.