Karshen taron Kungiyar kasashe Musulmi na dunia a Marroko | Labarai | DW | 09.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karshen taron Kungiyar kasashe Musulmi na dunia a Marroko

A birnin Raba na Marroko, an kamalla zaman taro, da ya hada ministoci 51, masu kulla da kananan yara a kasashe membobin kungiyar musulmi ta dunia.

Baban jigwan da mahalarta taron su ka tantana a kai, ya jibanci samar da matakan horra da yara, a game da tarbiyar addinin musulunci, da akidar zaman lahia, da wannan addini ke koyarwa.

Sanarwar karshen taron ta bukaci kasashe daban daban membobin kungiyar musulmi ta dunia, da su tabatar da kare hakokin yara, ba tare da nuna wariya ba, ko wace iri.

Haka zalika sun yi baki gudam, a kan wajibcin matsa kaimi, wajen waye kan jama´a, ta hanyar wa´azi, bisa illolin cutar Sida da ke ciki gaba da yaduwa kamar wutar daji a kasashen musulmi.

A daya hannu taron, yayi Allah waddai, da auren cilas, da kaciyya, kokuma kungullum, da a yanzu haka, a wasu kasashen musulunci, a ke cigaba da yiwa yaya mata.