Karshen taron kasashen kungiyar kudu maso gabacin Asia ta ASEN | Labarai | DW | 14.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karshen taron kasashen kungiyar kudu maso gabacin Asia ta ASEN

A Kwalalampur na kasar Malaisia, an kammala taron koli, na kasashen kungiyar Asen, da ta hada kasashe 10 da ke kudu maso gabacin Asia.

Taron ya samu halartar wasu karin kasashe 6, wanda ba membobin ba, da su ka hada da Japon, China, Korea ta kudu, India, Australiya, da New Zellende, kokuma Nouvelle Zelande.

Shugaban kasar Rasha Vladmir Poutine, da shima ya je, a matsayin dan kallo, ya halarci zauren shawarwarin..

Wannan haduwa, da itace irin ta farko, tsakanin shuwagabanin kasasen wannan kungiya, ta cimma sakamako mai tasiri.

Baki daya, shugabanin,sun yanke shawara haduwa so guda, ko wace shekara, domin tantana batutuwan da su ka shafi tsaro, da kuma cinikaya tsakanin su.

A daya hannun, sun cimma nasara sasanta Praministan China, Wen Jiabao, da takwaran sa na Japon Junichiro Koizumi, kasashe 2, da a watanin baya, su ka fuskanci matsananciyar kyamar juna.