Karshen taron kasa da kasa na neman taimako ga Afghanistan | Labarai | DW | 02.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karshen taron kasa da kasa na neman taimako ga Afghanistan

A birnin London na Engla an kammalla taron kwanaki 2 na neman taimakon gina kasar Afghanistan.

A sakamakon wannan taro, kasashe masu hannu da shuni, sun dauki sabin alkawura na tallafa hukumomin Kabul su samu kuddaden hidda kasar daga halin da ta tsinci kanta a ciki, bayan shekaru 4 na yake yake, da haren haren kunar bakin wake.

A jimilce alkawuran kudaden da za a baiwa kasar, sun tashi dalla billiard kussan 11,a tsawaon shekaru 5 masu zuwa.

Ministan kudi na kasar Afghanisatan, Anwarrulah Ahady, da ya ke hira da manema labarai, ya bayana matukar gamsuwa, da wannan nasara.

Hakan na nuni inji shi, da kimar da Afghanistan ke da ita, a idon kasashen dunia.

Daga tsabar kudaden Amurika, ta yi alkawarin dalla billiar 4, Bankin Dunia ta alkawarta dalla biliar 1 da milion dubu 2, sannan bankin raya kasashen Asia biliar daya, sai kuma Engla ta ambata taimakawa da dalla million 885, Jamus ta ware dalla 480.

Daga korar yan taliban daga karagar mulkin Afghanistan, ya zuwa yanzu,taimakon da kasar ta samu, daga ketare ya kai dalla billiyar 30 daidai.

Saidai kasashen sunngindayya sharrudan hukumomin wannan kasa sun maida himma, ta hanyar shinfida tsarin Demokradiya, da kare hakkoki bani adama, da kuma yaki da mugunyar sana´ar opium.