1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karshen mulkin rikon kwarya a Burkina Faso

Richard Tiéné/Salissou BoukariDecember 28, 2015

A daidai lokacin da ake bukukuwan nadin sabon shugaban kasar Burkina Faso, wasu 'yan kasar na tsokaci kan matakan da gwamnati da ke barin gado ta dauka.

https://p.dw.com/p/1HUcf
Burkina Faso neue Regierung in Ouagadougou Gruppenfoto
Hoto: STR/AFP/Getty Images

Daga cikin ayyukan da gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Burkina Faso a karkashin jagorancin shugaba Michel Kafando ta yi, akwai batun kwaskware kundin tsarin mulkin kasar, tare da sanya dan makulli ga batun takaita wa'adin takara ta yadda wani ba zai iya yin tazarce bayan cikar wa'adinsa ba. Akwai kuma batun kisan tsofon shugaban kasar Thomas Sankara, da ma na dan jaridar nan Norbert Zongo, ga batun aike takardar sammaci na tsofon shugaban kasar Blaise Compaore da a halin yanzu yake gudun hijira a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire. Ana iya cewa gwamnatin rikon kwaryar ta taka rawar gani, sai dai kuma wasu na ganin ta ba ta yi rawarta da tsalle. Evariste Konstin Koncebo shi ne shugaban wata kungiyar da ake kira "Cercle d'éveil ya tsokaci a kai...

Burkina Faso Präsidentschaftswahlen Halidou Ouedraogo
Hoto: DW/K. Gänsler

" Na farko dai akwai batun kara wa tsofon Firaminista Isaac Yacouba Zida girma wanda daga Laftanan kanal ya koma Janar duk kuwa da kashedin da rundunar sojan kasar ta yi, kuma a yayin taron majalisar ministocinsu na karshe an yi jimillan kwangiloli da suka bayar na wajen miliyan dubu hamsin. Lalle ga gwamnatin da ta kawo karshe abun tambaya ne, domin miliyan dubu hamsin ba karamin abu ba ne. Akwai kuma wasu nade-nade da aka yi ta yi wadanda ba su dace ba musali na jakadojin kasashe wanda ake ganin duk wannan ayyuka ne na sabon shugaban kasa, ga kuma wasu lambobin yabo da aka baiwa wasu"

A bukukuwan ranar 11 ga watan Disamba da ta gabata, da ta kasance ranar samun mulkin kan kasar ta Burkina Faso, an bai wa jagororin kungiyar Balai Citoyen lambobin yabo. Duk da ana ma ta kallon ta kusa da hukumomin rikon kwaryar, wannan kungiya ta ce ta na nan kan bakanta na mai tsaron gida, inda ta nuna adawarta ga nadin da aka yi wa Laftanan kanal Isaac Yakouba Zida a matsayin janar. A cewar Smokey daya daga cikin mambobin wannan kungiya ta balai citoyen shekara mai zuwa ta 2016 za ta kasance mai wahalar gaske ga Burkina Faso.

Burkina Faso Spannungen Präsidentengarde
Hoto: picture-alliance/Ahmed Ouoba/Panapress

" Wannan nadi ne na banza da wofi aka yi masa, kuma nadi ne da zai kara dagula harkoki a nan gaba, abun da ake so shi ne idan ka zo karshen aiki ka yi abun azo a gani ta yadda za ka tafi ana begen ka, amma sai kawai suka bata rawarsu da tsalle, don haka wannan shekara mai zuwa, za ta kasance mai wahalar gaske ga al'ummar wannan kasa, da kuma kungiyoyin hararan hulla masu fafutuka."

Ministoci da sauran 'yan majalisu na iya cin gajiyar wannan mulki na rikon kwarya, sai dai a nan babbar ayar tambaya ita ce, wai shin duk wadannan shawarwari an yankesu ne tare da sabon shugaban kasar Roch marc Christian Kaboré?