1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karshen gasar Olympics na birnin London

August 12, 2012

Amirka ce a sahun farko wajen lashe lambobi a gasar wasannin Olympics da Birtaniya ta yi amfani da ita wajen neman warware matsalar yunwa.

https://p.dw.com/p/15oSt
World Hunger Summit. Prime Minister David Cameron with newly crowned double Olympic champion Mo Farah (right) outside 10 Downing Street in London for the hunger summit photocall. Picture date: Sunday August 12, 2012. The Somalia-born athlete has been invited to join international politicians and other sporting greats at the event which is designed to shine the spotlight of the Games on the issue of child malnutrition. See PA story OLYMPICS Hunger. Photo credit should read: Max Nash/PA Wire URN:14294457
Cameron (hagu) yayin taron yunwa a karshen OlympicsHoto: picture alliance/empics

A yayin da ake kammala gasar wasannin Olympics da birnin London na Birtaniya ya karbi baƙunci, ƙasashen da suka taka rawar gani na bayyana farin cikin su game da yawan lambobin yabon da suka samu, inda waɗanda ba su taɓuka abin a zo a gani ba kuwa ke komawa ƙasashen su domin sake shiri da nufin tinkarar gasar ta gaba. Amirka ce dai ke sahun farko, inda ta sami lambobin Zinare da Azurfa da kuma Tagulla da ywansu yakai 104. Sai ƙasar China da ke rufa mata baya da yawan lambobi 87. Birtaniya - mai masauƙin baƙi kuwa ita ce ta zo ta ukku ta lambobin Zinare da Azurfa da kuma Tagullan da suka kai 65. A jerin ƙasashen Afirka kuwa Afirka Ta Kudu da Ethiopia dakuma Kenya ne suka fi nuna bajinta a lokacin gasar wasannin na Olympics na bana, bayan fitar da saamakon wasanni har 302 da aka fafata a lokacin gasar.

A halin da ake ciki kuma, ɗan asalin ƙasar Somaliyan nan, Mo Farah wanda ya ciwo wa Birtaniya lambar Zinare a gasar Olympics na bana a tseren mita 5,000 ya tallafa wajen ƙaddamar da babban taron daya shafi yunwa a duniya da nufin shawo kan matsalar rashin abinci mai gina jiki a sassa daban daban na duniya da fadar firayi ministan Birtaniya David Cameron ya karɓi baƙunci.

Farah, ya bi sahun Cameron da fitaccen ɗan wasan Brazil Pele da kuma fitaccen ɗan tseren Ethiopia Haile Gebrselassie da kuma mataimakin shugaban Brazil Michel Temer wajen karɓar baƙuncin taron, wanda yayi amfani damar Olympics ɗin wajen yunƙurin tallafawa ƙananan yara miliyan 25 dake fama da ƙarancin abinci mai gina jiki a duniya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal