KarramaThulisile Madonsela ′yar fafutka a Afirka ta kudu | Zamantakewa | DW | 23.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

KarramaThulisile Madonsela 'yar fafutka a Afirka ta kudu

Gidauniyar Afirka a Jamus ta karrama Jarumar yaki da cin hanci a Afirka ta Kudu Thulisile Madonsela tsohuwar mai gabatar da kara ta kasar da ta bankado badakalar kudi da Shugaba Zuma ya aikata.

A wannan Laraba ce gidauniyar Afirka a Jamus ta karrama Jarumar yaki da cin hanci a Afirka ta Kudu Thulisile Madonsela tsohuwar mai gabatar da kara ta kasar ta Afirka ta kudu. Sunan jarumar 'yan gwagwarmaya ya fita ne a duniya a sakamakon fito da rahoton badakalar rub da ciki da Shugaba Jacob Zuma ya yi a kasar. 

Ita dai Thulisile Madonsela ko kuma Thuli kamar yadda ake kiranta, shekaru bakwai ta yi tana rike da mukamin mai gabatar kara na kasar Afirka ta Kudu, kuma kamar yadda ta fada wa tashar DW dama can tun tana 'yar yarinya take da burin kawo sauyi a harkokin shari'ar kasarta ta haifuwa. ganin yadda ake samun kotuna da murda shari'o'in da suka shafi cin hanci.


"Ina tunawa lokacin da na mika takardar bukatar a biya mini karatun jami'a, sai na ce ina son karanta fannin shari'a, donmin na kawo sauyin dokokin kasarmu. A lokacin ina 'yar shekaru 16 da haifuwa, kuma abin da ya ja hankalina shi ne zanga-zangar masu adawa da wariyar jinsi da aka yi a wancan lokacin. A wannan lokacin na yanke shawarar cewa lallai zan yi karatun sanin yadda al'amura ke faruwa duniya, na ce mi za mu iya yi don sauya duk abin da muke ganin ba ma son aikata shi"

 

Jarumar a yaki da cin hanci dai ta fuskanci barazana iri-iri bisa fadin gaskiya kan aikinta, inda a wasu lokutan har aka yi barazanar hallakata, amma duk bai sa gwiwarta yin sanyi ba. Hasalima Madonsela kamar ana kara zugata ne. Tun fara aikinta aka fara gano wasu kumbiya-kumbiya da ake yi kan cin hanci, kuma a nan take 'yan kasar dama duniya suka fara sanin irin badakalar kudaden da Shugaba Jacob Zuma ya yi, kama daga miliyoyin kudin haraji da kuma yin amfani da kamfanoninsa don arzurta kansa. 'Yan kasar Afirka ta Kudu da sun yi ta jinjinamata, kamar yadda aka ji Trevo Tutu, dan Desmond Tutu yana mai cewa.

 

"Ita mace ta daban ce ta ko wane fanni. Kamarta ya kamata duk 'Yan kasarmu ta Afrika ta Kudu su kansance"

 

Itama dai kidauniyar Nelson Mandela, ta jinjina wa Madonsela bisa jajurcewar da ta yi wajen kare kundin tsarinn mulkin kasar, tamkar na mazan jiya irin su Mandela. Binceken da ta yi da ya kai ga bankado cin hanci, ya jawo boren dalibai da sauran al-ummar kasar.Wannan ce ta sanya wasu 'yan kasar Afirka ta Kudu ke cewa kamata ya yi Thulisile Madonsela, ta tsaya takarar neman shugabancin kasar. To amma kamar yadda ta shaida wa DW shugabancin kasa a yanzu ba shi ne a gabanta ba.


"Ina shirin samun karin dama ta tattauna da talakawa, domin ya taimakamin shigar da jama'a su dau matakan kare hakkinsu. Domin na yi aiki da mutane don tabbatar da kundin tsarin mulki ya yi aiki ga 'yan kasa ta ko wane fanni"

 

A lokacin da take rike da mukamin mai gabatar da kara dai ta yi gagarumin aikin da ba a taba ganinsa ba tarihin kasar, inda take da ma'aikata 300 karkashinta, kuma ta tarar da kararraki kimanin dubu 40, kuma kafin ta bar aikin na tsawon shekaru bakwai da ta yi Thulisile Madonsela, ta kammala aikin kararraki kimanin dubu 30.000 abin da ba a taba gani ba. Cikin bankado muna-muna da cuwa-cuwa da ta yi har da yadda ake rub da ciki kan kudin tallafin karatun dalibai, da yin cuta wajen biyan kudin fansho ga tsaffin ma'aikata da dai sauransu.