1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karo - karo a Jamus.

YAHAYA AHMEDNovember 24, 2005

Idan aka zo ga batun ba da gudummuwa ta hanyar karo karo ga wadanda annoba ta shafa, Jamusawa ne kan gaba a jerin kasashen nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/BvUG
Kasuwar kirismeti
Kasuwar kirismetiHoto: AP

A halin yanzu dai, an fara hidimomin kirismeti a nan Jamus, kusan makwanni 4 kafin ranar bikin. A ko’ina, za a iya ganin rumfunan da aka kakkafa na kasuwar kirismeti, wadda wata al’ada ce a nan Jamus ta sayad da kayayyakin alatu da kyaututtuka na shirye-shiryen bikin. A wannan lokacin ne kuma, kungiyoyin sa kai da dama ke ta aikewa da takrdun neman taimako daga jama’a, don tallafa wa yara masu fama da matsaloli da cututtuka a kasashen Latinamirka da kuma nahiyar Afirka. daya daga cikin kungiyoyin suka fi ba da kaimi wajen neman taimako a wannan lokacin ita ce kungiyar nan ta Adveniat, ta wani rukunin bishop-bishop na cocin katolika. Jami’in kungiyar mai kula da dangantaka da jama’a, Christian Frevel, ya bayyana cewa:-

„Kalmar Adveniat din dai daga Latin take, kuma ma’anarta ce Daularka ta zo gare mu. A lokacin kirismeti ne dai muka fi ba da kaimi a aikinmu. Saboda wannan lokacin bisa al’ada, lokaci ne na nuna zumunci da raba duk kwantan da mutum ke da shi, da marasa galihu. A nan kasar kuwa jama’a na amsa kiran da muke yi musu sosai. kungiyar Adveniat dai, ita ce kungiya ta biyar da jama’a suka fi ba ta tallafi a nan Jamus, don gudanad da aikinta.“

Bana dai, a ran 27 ga wannan watan ne kungiyar ta cocin katolika, za ta fara neman karo-karon da take yi a wannan lokacin. kasar da ta zaba tamkar jigonta na wannan shekarar, ita ce Brazil. Akwai dai wurae da dama a duniya, inda aka fi bukatar taimako da kasar Brazil. Amma, ita kungiyar ta Adveniat, tana dukufad da mafi yawan aikinta ne ga yankin Latinamirka. A ganin Bernd Beder, shugaban hukumar sa ido kan kungiyoyin sa kai a nan Jamus, dukufad da aikinta da Adveniat ta yi a Latinamirka na da fa’ida kwarai da gaske. Saboda a ko yaushe mutane suka ba da gudummowa, sun san abin da ake yi da kudinsu.

A bangare daya kuma, yawan annobar da aka yi ta samu a wannan shekarar, sun sa masu ba da gudummowar ma sun nuna alamun gajiya ko kuma hasala, inji Beder. daya daga cikin dalilan da ya sa ke nan, ake huskantar matsala wajen tara isassun kudaden taimako ga wadanda girgizar kasar nan ta Pakistan ta shafa.

Duk da cewa, taimakon kudaden da ake samu bai ragu ba kamar yadda ake fargaba, akwai masu nuna damuwarsu ga yadda ababa za su kasance nan gaba.