1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karl Marx ya cika shekaru 200

Suleiman Babayo | Abdul-raheem Hassan
May 8, 2018

Masanin falsafa dan Adam dan asalin Jamus ya kasance daya daga cikin fitattun masana a duniya, wanda rubuce-rubucensa da ya yi suka ci gaba da tasiri har yanzu.

https://p.dw.com/p/2xMIn
Enthüllung Karl-Marx-Statue in Trier
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Probst

Za a iya cewa ya zama mutum mafi tasiri na falsafa da aka samu a tsawon tarihin Jamus, an haifi Marigayi Karl Marx a 1818 a karamin garin Trier. Tun yana da kananan shekaru yake gwagwarmaya da masu ra'ayin sauyi na lokacinsa. Domin haka ya yi hijira zuwa birnin Paris na Faransa da London na Birtaniya. A London Marx ya mayar da hankali kan matsanancin yanayin da ma'aikata ke ciki, wadanda ke karkashin tsarin kashin dankali a farko fara aiki da tsarin jari hujja.

Manufofin tsarin Gurguzu

Karl Marx ya rubuta manufofin tsarin gurguzu a shekarar 1847 tare da abokin aikinsa Friedrich Engels bisa neman samar da dama iri guda ga kowa. Richard Löwenthal na zama masanin siyasa da ke Jamus: Ya ce

UK Grabmal von Karl Marx in London
Mutum mutumin Karl Max a birnin LandanHoto: picture-alliance/akg-images

"Gagarumar gudunmawar Marx ta kasance bisa sanin da yake da shi game da kimiya da ya janyo ma'aikata tashi tsaye game kamar yadda ake samu a addini. Abin da ka iya zama hadarin saboda yadda yake zama a zuciyar wadanda suka yi imani da haka."

Daga bisani Marigayi Karl Marx ya yi rubutu kan tsarin jari hujja, wannan ya zama tubalin tsarin gurguzu, kuma daga baya ana kiran aikin Lenin, Stalin, Mao Tse Tung wadanda suka gina mulkin kama karya da sunan Karl Marx.

Tasirin rubuce-rubucen Karl Max bayan mutuwarsa

Bayan rayuwar samanin falsafan daga garin Trier bai san irin tasirin da aikinsa ya yi ba. Amma 'yan gurguzu sun yi kaurin suna na tsawon shekaru. Yanzu shekaru 30 bayan tsarin gurguzu lamura suka fara inganta. Martin Endreß, masanin halayyen dan Adam na Jami'ar garin na Trier. Yace:

Deutschland Marx-Statue in Trier
Mutum mutumin Karl Marx a garin Trier na JamusHoto: picture-alliance/dpa/H. Tittel

"Shekarun tsatstsauran ra'ayi' haka masanin tarihi Eric Hobsbawm ya kira karni na 20 daga ya shude. Bayan shekarar 1989 an sake sakin manufar Marx. Tun lokacin binceke kan fannoni da dama sun karfafa babu iyaka kan gasa. Kuma haka bai tsaya ga manufofin siyasa da yadda Marx ya yi tasbihi."

Gwagwarmayar samar da 'yanci

Shi dai Karl Marx baya ga zama masani ya kuma kasance fitaccen marubuci musamman la'akari da rubutun tsarin gurguzu da ya yi, abin da zai iya tsayuwa a yanzu haka bisa zaiyana tsarin danniya da rashin adalci, ba wai a kasashen Turai kadai ba har sauran kasashen duniya.

Murnar cika shekaru 200 na Karl Marx a garin haihuwarsa

Ana bikin cika shekaru 200 da haihuwa Karl Marx a wannan lokaci cikin nishadi a kasar Jamus, domin ana fahimtar cewa ba komai da aka aikata da sunansa ne ya amince ba. Saboda bayan rasuwarsa ba yi da ikon kare aikin da ya yi daga amfani da shi ta wata hanya.