Kariyar doka ga matalauta | Siyasa | DW | 22.01.2010
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kariyar doka ga matalauta

Kimamin mutane miliyan dubu huɗu a faɗin duniya ba sa samun wata kariya ta doka ko shari´a

default

Monika Lüke shugabar Amnesty International reshen Jamus

To sai dai samun irin wannan kariya wani ginshiƙi ne mai muhimmancin ga ´yancin ɗan Adam na yaƙi da talauci. Sai an bawa talakawa cikakken ´yancinsu ne za su samu damar kare kansu. Akan wannan batun ne ƙungiyar Amnesty International reshen Jamus ta kira wani babban taron ƙasa da ƙasa inda limaman coci da ´yan radin kare haƙƙin Bil Adama da kuma ƙwararrun masana suka yi musayar yawu.

Sau da yawa rashin kuɗi da ilimi na kawo ciƙas wajen shiryawa tare da aiwatar da wani ƙara da zai yi nasara. Kuma idan a ƙarshe mutane a cikin talauci suka ɗaukaka ƙara a kotu, shari´ar na ɗaukar lokaci mai tsawo ko kuma ba a mutunta wannan hukunci. Ba a ƙasashe mataulata kaɗai ba, hatta a nan Jamus ƙungiyoyin taimakawa jama´a na ƙorafin cewa ba kullum ne kotu ke yiwa talakawa adalci ba.

Babbar sakatariyar ƙungiyar Amnesty International reshen Jamus, Monika Lüke ta yi bayanin dalilan da suka sa ƙungiyarta ke mayar da hankali kan wannan batu.

"Sau tari ana haɗa talauci da batun kare haƙƙin ɗan Adam. Cin zarafin ɗan Adam kan jefa mutane cikin talauci sannan a lokuta da dama talakawa ne ake take haƙƙinsu fiye da sauran mutane."

´Yancin samun muhalli na daga cikin haƙƙoƙin jin daɗin jama´a. A nan sakatariyar ta Amnesty a Jamus ta ba da misali da ƙasar Angola, inda a watan Oktoban shekara ta 2008, cikin dare ɗaya daruruwan mutane suka rasa gidajensu bayan jami´an tsaro sun fatattakesu da ƙarfin tuwo.

David Mendes yana aiki ne a ƙungiyar Maos Livres ta lauyoyi da ´yan jarida dake kare haƙƙin jama´a a birnin Luanda ya ce ƙungiyar na ƙoƙarin hana tilasta mutane barin gidajensu.

"A cikin kundin tsarin mulkin Angola an yi magana game da daidaita ´yanci wato  duk ´yan ƙasar ɗaya suke a gaban shari´a. Tsarin mulki ya tabbatarwa ´yan ƙasa damar ɗaukaka ƙara kan wani hukuncin da ba a yi adalci a ciki ba."

To sai dai babu wani ingantaccen tsari da ƙasar ta Angola ta yi na aiwatar da wannan doka musamman saboda cin hanci da rashawa da suka zama ruwan dare a ƙasar.

A ta bakin Michael Windfuhr na ƙungiyar coci masu taimakawa jama´a, rikice-rikice kan ƙasa ko fili na ɗaukar lokaci mai tsawo a gaban kotu. Ya ba da misali da ƙasar Indiya inda yanzu haka akwai irin waɗannan ƙararraki har miliyan 38 kan rikicin filaye. Akan ɗauki kimanin shekaru 10 kafin a gama shari´a guda ɗaya.

Wata matsalar kuma ita ce ta rashin isasshen abinci musamman ga ƙananan yara, inda a wasu ƙasashen kamar Indiya an kasa gabatar da wata doka wadda za ta tabbatar da ´yancin jama´a na samun isasshen abin sakawa bakin salati.

Shugabar Amnesty a Jamus Monika Lüke ta ce daga cikin matakan da ya kamata a ɗauka don kai gaci shi ne wajen ba da taimakon raya ƙasa ya kamata a ƙarfafa yiwa tsarin shari´a kwaskwarima don bawa mutane damar amfani da ´yancinsu.

Malcolm Langford na cibiyar kare haƙin ɗan Adam ta ƙasar Norway ya yi nuni da wasu ƙasashe da suka bi sahun Indiya wajen ɗaukar matakai na gama gari.

"Alal misali kimanin shekaru biyu da suka wuce tarayyar Najeriya ta yiwa kundin tsarin mulkinta kwaskwarima don ba da damar ɗaukar matakai na gama gari."

Mawallafa: Sabine Ripperger/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Ahmad Tijani Lawal

 • Kwanan wata 22.01.2010
 • Mawallafi Mohammad Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/LelG
 • Kwanan wata 22.01.2010
 • Mawallafi Mohammad Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/LelG