Karin jami´an hukumar IAEA sun isa kasar Koriya Ta Arewa | Labarai | DW | 28.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karin jami´an hukumar IAEA sun isa kasar Koriya Ta Arewa

Wasu karin sifetoci na hukumar kulada makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA sun isa a kasar KTA inda zasu sa ido a aikin rufe tashar nukiliya ta Yongbyon. Shugaban tawagar ya ce kwararrun su 6 zasu maye gurbin wasu sifetocin hukumar wadanda suke kasar ta KTA tun kimanin makonni biyu da suka wuce. Hukumomin birnin Pyongyang sun nuna shirin yin watsi da shirin nukiliyar KTA da ake takaddama a kai, yayin da za´a sakawa wannan kasa da taimakon tattalin arziki da na jin kai.