Karin bayani game da dutsen Everest
June 17, 2013
Dutsen Everest ya na tsakanin kasashen Nepal da kuma China a yankin Tibet.
Babu shakka shi ne Dutse ko tsauni wanda ya fi ko wane tsawo a duniya, tsawansa ya kai mita 8848, wato kusan kilomita Tara. A karon farko turawan sun gano wannan dutse a shekara 1847, shekaru 166 kenan da suka gabata.
Tun daga shekara 1922 masu yawan bude ido su ka fara hawa kan dutsin, inda wasu daga ciki su ka yi nasara kaiwa kololuwarsa.
Daga shekara 1922 zuwa yanzu fiye da 'yan yawan bude ido dubu 14 su ka jaraba hawan wannan dutse, wasu sun yi nasara kaiwa har makura a yayin da wasu kuma su ka kasa. Alkalumma sun ce mutane dubu hudu suka yi nasara kaiwa makurar Dutsen Everest.
Mutune biyu ne suka yi nasara kaiwa a karon farko ga makurar dutsin, sune: Edmund Hillary na kasar Newzeland da kuma Sherpa Tenzing Norgay, sun kai makurar Everest ranar 29 ga watan Mayu na shekara 1953 a karfe 11.30 na rana.
A lokacin Edmund Hillary bayan ya sauko kasa, ya baiyana gamsuwa, ga abin da yake cewa:
"Na gamsu matuka da wannan nasara da na samu. Mutane da dama kamin ni sun jaraba kaiwa koluluwar wannan dutse ba su yi nasara ba."
Game da tsawan lokacin da ake kamin aiwa ga mukara dutsen, ya dangata daga masu hawan. Aiki ne mai tattare da hadarin gaske, saboda haka ne da dama daga mutanen su ke amfani da na'urar da ke taimaka masu wajen shedawa.Kiddidiga ta gano cewa daga shekara 1922 da aka fara hawan wannan dutse fiye da mutane 200 su ka rasa rayuka.
Ya zuwa yanzu, wasu 'yan kasar Swizland, wato Erhard Loretan da Jean Troillet su ne su ka fi kowa sauri wajen hawa da sabkowa daga Dutsen Everest.A jimilce, sun yi sa'o'i 43 ba tare da sun yi amfani ba da na'ura mai taimaka masu wajen shedawa.
Amma akwai wanda ba su dauki tsawan sa'o'i 43 ba, to sai dai sun yi amfani ne da na'ura mai taimakawa sheda.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal