Karfin katanga ko kuma shinge
A yayin da ake fama da matsalar bakin haure, kasashen Turai na ci gaba da gina shingaye a kan iyakokinsu, abin da ake ya yi a duniya. Ba kamar katangar Berlin ba, ana sanya shingen domin hana bakin hauren shiga.
Kasashen Schengen sun rufe kan iyakokinsu
Gwamnatin kasar Hangari karkashin jagorancin Firaminista Viktor Orban, ta kafa shinge a kan iyakarta da Sabiya kana ta fara kafa wani a kan iyakarta da makwabciyarta Kwuroshiya, wadda ke cikin kungiyar EU. Da yawa cikin 'yan gudun hijirar da ke fitowa daga Girka su biyo ta kasashen yankin Balkan, na son shiga Ostiriya da Jamus.
Melilla - Sansanin sojojin Turai
Kan iyakar tsibiran Melilla da Ceuta, mallakar kasar Spain da ke Maroko, na zaman kan iyakar da ya fi ko wanne tsaro a duniya. An zagaye biranen da shinge mai tsahon mita shida. An sa masa dannin waya da kyamarori da kuma na'urar sansano sauti. An gina wadannan shingaye domin hana 'yan gudun hijira daga Afirka tsallakawa Turai.
Rababben Tsibiri
Yankin da aka sani da Cyprus "Green Line" na kunshe da shinge mai dauke da dannin waya da barakuzai da hasumiyar hangen nesa da kuma yankin katanga. Daga kimanin tsahon kilomita 180, shingen ya raba Tsibirin bangaren Turkiya daga arewa da kuma bangaren Girka daga Kudu. Dubban sojoji na gadin ko wanne bangare, Nicosia ne birnin da ya rage a rabe a duniya tun bayan faduwar katangar Berlin
Katangar Tortilla
Kimanin 'yan sandan tsaron kan iyaka na Amirka 20,000 ne ke gadin kan iyakar Amirka da Mexiko. Katangar Tortilla na da tsahon kilomita 1,100. Tsarin kula da kan iyakar na amfani da bidiyo da kyamarori da na'urar hange da daddare da kuma ta sansano motsi da taku. An gina katangar ne domin hana shiga kasar ta barauniyar hanya.
Kasa mai tsarki- ta rabu gida biyu
Gurin bincike kalilan ne a kan hanyar tsallaka kan iyakar Isra'ila da Falasdinu, kamar a nan birnin Kudus. An gina katangar ne domin kaucewa hare-haren Falasdinawa. Sai dai duk da kan iyakar da masu tsaronta, Falasdinawa na yankin Zirin Gaza na samun damar shiga da makamai da sauran kayan masarufi ta hanyoyin karkashin kasa da suka haka da kansu.
Yankin Koriya da babu sojoji a ciki
Ana ganin ta a matsayin kan iyakar da ta fi tsaro a duniya. Dannin waya da hasumiyoyi masu hangen nesa sun raba kasashen Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa mai mulkin 'yan mazan jiya. Mai fadin kilomita hudu, yankin da ba sojoji a cikinsa an haramta shiga ko wanne bangare na kan iyakar da ke da tsahon kilomita 248. An gina katangar bayan kawo karshen yakin kasashen Koriya a shekara ta 1953.
Yankin zaman lafiya na Ireland ta Arewa
Yankunan zaman lafiya 48 ne suka raba 'yan Protestant daga makwabtansu 'yan Katolika a Ireland ta Arewa. A Belfast babban birnin kasar, akwai shingaye da ke da katanga mai tsahon mita bakwai, wadda aka gina da dannin wayoyi da bulo da kuma dakin na kankare. Katangar na da hanya da masu tafiya a kasa ke wucewa da kuma kofar da masu motoci ke bi. Ana rufe kofofin da daddare.
Babban shingen Indiya
Kan iyakar da ta fi tsaho a duniya. Indiya na amfani da danni waya na kilomita 4,000 domin rufe kan iyakarta da Bangaladash, kasar da ake wa kallon maboyar 'yan ta'adda. Kan iyakar na da tsahon mita biyu, an kuma sanya wayoyi domin karfafa shingen. Kimanin sojoji 50,000 ke lura da kan iyakar.
Katangar Berlin - Bangon da ya fadi
Katangar Berlin na da tarihi a duniya. An santa a matsayin tarkon mutuwa, ta fadi a ranar tara ga watan Nuwamba na 1989. Faduwar katangar ya kawo karshen yakin cacar baka, Jamus ta sake hadewa. Sai dai duk da dinbin darasin da ke cikin tarihin katangar, bai janyo hankalin sauran kasashen duniya sun kaucewa gina irin wannan katangar tare da ware kansu ba.