1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa matakan tsaro a Britania

July 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuHS

Jamian yan sanda a Britania sun sanar da cafke karin mutane biyu,wadanda ake zargi da hannu a harin tarzoma da aka kai filin saukan jiragen sama na Glasgow,kana da yunkurin kaiwa birnin london hari.Cafke wadannan mutanen guda biyu da akayi a yankin arewacin kasar,ya kawo ga adadin mutane 4 kenan aka kama kawo yanzu.Jamian tsaro a Britanian dai sunyi tsayuwar daka,domin tabbatar da tsaro a fadin kasar bisa barazanar hari irin na taaddanci.Sakatariyar harkokin cikin gida na Britania jacqui Smith ta bayyana cewa,ta karfafa matakan tsaro a sassan kasar sakamakon ababan da suka faru a a biranen London da Scotland cikin tsukin kwanaki biyu da suka gabata.