1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karfafa dangantakar Jamus da China

March 28, 2014

A wani mataki na sake karfafa dangantakar dake tsakanin Jamus da kasar China shugaban kasar China Xi Jinping ya iso nan Jamus domin ziyarar aiki ta kwanaki biyu.

https://p.dw.com/p/1BXre
Hoto: Reuters

Wannan dai shine karo na uku da Shugaba Xi Jinping na China ya kawo ziyara nahiyar Turai sai dai kuma shine karo na farko da ya ziyarci Jamus kasar dake zaman mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Turai din tun bayan darewarsa kan karagar mulki a shekarar da ta gabata. A yayin ziyarar tasa dai ana sa ran kasashen biyu za su kulla yarjejeniyar kasuwanci da fannin tsaro na makudan kudade.

Shugaba Xi dai na samun rakiyar matarsa ne Peng Liyuan inda suka samu tarba daga Shugaban kasar Jamus din Joachim Gauck a lokacin da suka sauka a filin saukan jiragen saman birnin Berlin. Baya ga saka hannu a kan yarjejeniyar kasuwanci ta dubban biliyoyin Euro, wani abu da ake sa ran zai mamaye ganawar ta su shi ne batun tsaro da kuma na Ukraine biyo bayan mamayar da kasashen yammam ke ganin Rashan ta yi wa yankin Kirimiya na Ukraine din. Ana kuma sa ran Shugaba Xi zai gana da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a yayin ziyarar tasa.

Kimanin magoya bayan yankin Tibet 50 ne dai suka gudanar da zanga-zangar lumana a bakin fadar gwamnatin Jamus domin nuna adawarsu kan matakin da China ke dauka a kan yankin.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Auwal Balarabe